<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Bliss, Philip Paul (1838-1876)</author>
<title>Zaɓaɓɓe Na Allah, Shi LW589</title>
<lyrics>[V1]
 1) Zaɓaɓɓe na Allah, shi
 Aikkake na ainihi
 Nufin Allah duk yayi,
 Ubangiji, Almasihu.

[V2]
 2) Yesu aka kunyata
 &quot;Shi ba wani abu ba,&quot;
 Aka ce. Ai, shi ya sa
 Aka raina Almasihu.

[V3]
 3) Shi a jikin gungume
 Ga shi nan kwa, ɗaurarre!
 Aka kashe shi sosai,
 Mai Alheri ne ya mutu.

[V4]
 4) Mutumcinsa aka ci,
 Zub da jini aka yi,
 Karɓar ceto aka ƙi,
 Jinin Yesu ya panshe mu.

[V5]
 5) Riƙe shi ba dama fa
 Ko a wurin mutuwa,
 Allah ma ya ɗaukaka
 Ɗansa, Yesu Almasihu.

[V6]
 6) In ya komo wata rana,
 Zai tashe mu daga nan.
 Har ya kai mu gun Uban,
 Rerawa mu yi ma Yesu.</lyrics>
<hymn_number>589</hymn_number>
</song>